Sinopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodios
-
Shirye-shirye na musamman kan tarihin zuwan Turawa ƙasar Hausa
17/09/2024 Duración: 09minShirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al’ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......
-
Jerin shirye-shirye kan tarihin zaman takewar ƙasar Hausa kafin zuwan Turawa
10/09/2024 Duración: 09minShirin a wannan makon ya maida hankali ne yadda tsarin shugabanci ya ke a kasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
-
Yaya tsarin tafiyar da mulki yake a ƙasar Hausa kafin zuwan turawa
27/08/2024 Duración: 09minShirin na wannan mako ya duba irin tasirin masu mulki a ƙasar Hausa kafin zuwan turawan Mulkin mallaka Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani
-
Yadda sana'ar ƙira ke gushewar a al'adar ƙasar Hausa
13/08/2024 Duración: 09minA yau shirin za ya kai mu Jamhuriyar Nijar, musaman jihar Maradi.A wannan yankin na Maradi a garin Radi, zamu duba batun kirar gargajiya da ke kan hanyar bacewa, bayan a can baya kira, wanzamci, sun kasance sana’o’i biyu da ake alfahari da su a cikin gari. A dauri, makeri baya noma a irin wannan lokaci na damina, sai dai ya yi ta aikin kera kayan noma da gyaransu idan sun lalace, idan kaka ta yi dukan manoma sai su hada masa dammuna hatsi, irin su dawa ko ma wake da zai kula da iyalinsa.