Wasanni

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:59:11
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Episodios

  • Salah ya shafe tarihin Thierry Henry na yawan jefa kwallo a gasar Firimiya

    27/01/2025 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya ziyarci gasar Firimiyar Ingila ne don duba sabon tarihin da ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah ya kafa a gasar. Mohammad Salah dai a yanzu ya shafe tarihin Thierry Henry na zura kwallaye 175 a gasar Firimiyar Ingila, bayan da ya jefa kwallo a karawar da suka yi da Ipswich. A yanzu dai Mohammed Salah ne na 7 a jerin ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a raga a babbar gasar ta Ingila.Ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a gasar dai su ne Alan Sheare mai  kwallaye 260 da Harry Kane  213 da Wayne Rooney 208 da Andrew Cole 187  da Sergio Agüero 184 da Frank Lampard 177 sai shi Mohamed Salah 176 ya yinda a yanzu Thierry Henry  mai kwallaye 175 ya koma mataki na 8 a wannan jeri.Ƙu latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........

  • Sharhi kan kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da Ademola Lookman ya lashe

    23/12/2024 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wassani a wannan makon ya yi duba ne game da kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da aka bayar. A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Hukumar da ke kula da kwallon ƙafar nahiyar Afrika wato CAF, ta bayar da kyautar gwarzon nahiyar Afrika wanda yafi bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Najeriya Ademola Lookman ne ya samu nasarar lashe wannan kyauta, biyo bayan irin bajintar da ya nuna ga ƙasar da kuma ƙungiyarsa ta Atlanta. Samun nasarar lashe wannan kyauta da ɗan wasan yayi dai ta sanya zamowa cikin jerin ƴan wasa 6 na Najeriya da a tarihi suka taɓa lashe ta.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh........

  • Sauye-sauyen da aka samu a bana a gasar wasan kokuwar gargajiya ta Nijar

    16/12/2024 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon, yayi duba ne game da gasar kokuwar gargajiya a Jamhuriyar Nijar, wacce za a faro a ranar 20 ga wannan wata na Disamba nan a jihar Dosso da ke rike da takobi ko kambun gasar, inda ƴan wasa 80 daga Jihohi 8 na Nijar za su fafata har zuwa 29 ga watan, don samun sabon sarkin ƴan kokuwa wanda ke lashe kyautar takobi da kuɗaɗe da sauran kyautuka. Sai dai wani hanzari da ba gudu ba shi ne yadda a bana aka samu wasu sabbin sauye-sauye musamman ɓangaren dokokin wannan gasa.Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh..........

  • Ƴan wasan lik ɗin Najeriya na fuskantar barazana sakamakon tafiye tafiye ta mota

    09/12/2024 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ƴan wasa a Lik din Najeriya ke fuskantar barazana a tafiye tafiye ta mota da suke yi don yin wasa. Yin amfani da motoci wajen jigilar ƴan wasan da ake fafatawa a gasar Lik ɗin Najeriya ba sabon abu bane, ganin yadda mafi yawancin ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa sun fi amfani da motoci wajen kai ƴan wasansu jihohin ko garuruwan da za su fafata wasa. Irin waɗan nan tafiye tafiye dai na haifar da barazana ga rayuwar ƴan wasan musamman idan aka yi la’akari da rashin ƙyaun hanyoyi ko kuma da kuma matsalar tsaro.Ƙungiyar El-Kenemi Warriors ce ta baya-bayan nan da ƴan wasanta suka fuskanci wannan barazana, a hanyar su ta koma birnin Maiduguri bayan buga wasan mako na 14 da suka yi Ikorodu City a birnin Lagos.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

página 2 de 2