Al'adun Gargajiya

Bikin cika shekara daya da sarkin Katsinar Maradi yayi da hawa kan karagar mulki

Informações:

Sinopsis

Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya maida hankali ne kan cika shekara daya da sabon sarkin Katsinar Maradi,Mai Martaba Ahmad Ali Zaki Maremawa yayi kan karagar mulki. A dai ranar Asabar 5 ga watan Nuwambar shekarar da ta gaba ne aka nada Mai Martaba  Ali Zaki a matsayin Sultan na 2 na Katsinar Maradi. Shirin ya tabo batun nasarorin da sarkin ya samu a wannan lokaci da yayi yana jagoranci.Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa....