Bakonmu A Yau

''Jami’an tsaron Najeriya sun cafke ‘yan ƙasashen waje da dama '' SP Abdull Haruna Kiyawa

Informações:

Sinopsis

Jami’an tsaron Najeriya sun cafke ‘yan ƙasar Poland 7, bisa tuhumarsu da yaɗawa gami da ɗaga tutocin Rasha a Kano, yayin zanga-zangar da dubban matasa suka gudanar kan tsadar rayuwa a faɗin ƙasar, da ta kai ga salwantar rayukan mutanen da kungiyar Amnesty ta ce adadinsu ya kai 20. Sanarwa daga rudunar tsaron Najeriya na bayyana cewa,kafin kamen dai, sai da jami’an tsaron Najeriyar suka cafke aƙalla mutane 30 saboda ɗaga tutocin Rasha da suka riƙa yi yayin zanga-zangar ta gama-gari, a wasu jihohin ƙasar ciki har da Kano.Kan haka Aisha Shehu Kabara ta tattauna da kakakin rundunar ‘Yan Sandan jihar Kano SP Abdull Haruna Kiyawa, wanda yayi ƙarin hake kan halin da ake ciki.