Bakonmu A Yau

Ahaji Umaru Dembo kan bukatar Ɗangote da wasu matatun mai na Najeriya

Informações:

Sinopsis

Katafariyar matatar man Ɗangote ta ce ita da wasu masu tace mai na cikin gida na bukatar akalla ganga dubu 600 na ɗanyen mai kowacce rana domin gudanar da ayyukansu, yayin da ƙasar ke samar da ganga miliyan guda da dubu 300 kowacce rana. Sai dai ga alama har yanzu matatun ba su kai ga samun biyan bukata ba, dole sai sun dogara ga wadanda suke shigo da shi daga kasashen ketare. Dangane da wannan batu ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon ministan albarkatun mai Ahaji Umaru Dembo.Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakkiyar hira da muka yi da shi.