Bakonmu A Yau

Wane hali ake ciki game da shigar da kayan abinci masu rahusa Najeriya

Informações:

Sinopsis

Kusan watanni 2 da bada umarnin shigar da abinci Najeriya ba tare da kudin fito ko haraji ba domin karya farashinsa da kuma wadata jama'a, amma har yanzu samar da abincin ya gagara. Rahotanni sun ce 'yan kasuwa sun kasa samun kudaden kasashen ketare domin sayo abincin daga kasashen duniya. Sanata Garba Musa Mai Doki, dan majalisar dattawa daga jihar Kebbi ya ce ya zama dole gwamnati ta shigo da abincin da kanta domin wadata jama'a da kuma rage musu radadin halin da suke ciki.Ga yadda tattaunawarsu ta gudana da Bashir Ibrahim Idris lokacin da ya ziyarci ofishinmu a Lagos.