Bakonmu A Yau

Prof Shehu Abdullahi Zuru kan binciken yadda ƴan Afrika basa jin daɗin mulkin dimukaradiya

Informações:

Sinopsis

Shugaban Gidauniyar Shehu Musa Yar Adua Akin Kekere-Ekun, ya bayyana cewar kashi 80 na jama'ar nahiyar Afirka ba sa jin daɗin yadda zaɓaɓɓun shugabanninsu ke tafiyar da mulkin dimukiraɗiya a ƙasashen su. Jami'in ya ce akwai wagegen giɓi tsakanin yadda shugabannin ke mulki da kuma buƙatun jama'a, musamman abinda ya shafi ayyukan da suke so. Dangane da binciken da Gidauniyar ta yi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze da ke Abuja. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........