Bakonmu A Yau

Alhaji Abubakar Maigandi kan tasirin daina sayarwa Ɗangote man fetur da Naira

Informações:

Sinopsis

Gidajen man fetur a Najeriya na ci gaba da sauya farashi, bayan da matatar Dangote ta sanar da cewa yarjejeniyar da ke tsakaninta da NNPC wadda ke bayar da damar samun gurbataccen mai a farashin Naira ta kawo ƙarshe ba tare da an sabunta ta ba. Alhaji Abubakar Maigandi, shugaban ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya wato IPAM, ya ce tuni suka yi hasashen faruwar hakan bayan rugujewar waccan yarjejeniyar.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.