Wasanni

Dalilan durkushewar manyan ƙungiyoyin Arewacin Najeriya da suka bada gudunmuwa a baya

Informações:

Sinopsis

Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimaka wa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A baya yankin Arewacin Najeriya ne ke kan gaba wajen samar da manyan ƴan wasan da ake ji dasu a ƙasar, kuma mafi yawancin ƴan wasan sun fito ne daga ƙungiyoyi na cikin gida irinsu DIC Bees da ke Kaduna wacce ta koma Ranchers Bees da Racca Rovers da ke Kano da Mighty Jets da ke garin Jos da dai sauransu. Sai dai shirin a wannan lokacin zai yada zango ne a jihar Kaduna, don yin duba a kan ƙungiyar DIC Bees, wacce Sanata Muktar Muhammad Aruwa ya saya a shekarun 1980, kuma ya sauya mata suna zuwa Ranchers Bees.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...........