Bakonmu A Yau

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 1:29:14
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Dokta Tijjani a kan rashin kataɓus na tawagar Najeriya a gasar Olympics

    13/08/2024 Duración: 03min

    Wasu 'yan Najeriya sun bukaci gwamnatin kasar da ta kaddamar da bincike domin gano dalilin da ya sa kasar ta kasa lashe koda tagulla guda a gasar Olympics da ya gudana a Paris, liura da makudan kudaden da aka kashe da kuma yawan 'yan wasan da kasar ta kai Paris. Domin duba wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Tijjani Yusuf, tsohon Darakta a hukumar wasannin Najeriya, kuma malami a Jami'ar Bayero dake Kano. Ga yadda zantawarsu ta gudana.

  • Farfesa Bello Bada kan taƙaddamar gwamna Lawal Dare da Bello Matawalle a Zamfara

    12/08/2024 Duración: 09min

    Mazauna Jihar Zamfara da ke Najeriya na ci gaba da bayyana damuwarsu a kan yadda rashin fahimtar juna tsakanin Gwamna Dauda Lawal da karamin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle ke ci gaba da zagon kasa ga shirin samar musu da tsaro a jihar. Dangane da wannan Faruk Muhammad Yabo ya tattauna da Farfesa Bello Bada na Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

  • Tattaunawa da Kashim Shettima kan halin da Najeriya ke ciki

    09/08/2024 Duración: 03min

    Al'umma Najeriya sun daɗe suna kukan cewa alamu na tabbatar da lallai gwamnati musamman shugaban ƙasa da mataimakinsa basu da masaniyar ainihin munin hali da talaka ke ciki tun bayan janye tallafin man fetur, wanda hakan yasa har aka kai ga zanga-zanga.  A tattaunawarsa da wakilinmu na Abuja Mohammed Sani Abubakar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bukaci ƴan Najeriya da su yi hakuri tare da karawa gwamnati lokaci don share musu hawayensu.

  • ''Jami’an tsaron Najeriya sun cafke ‘yan ƙasashen waje da dama '' SP Abdull Haruna Kiyawa

    08/08/2024 Duración: 03min

    Jami’an tsaron Najeriya sun cafke ‘yan ƙasar Poland 7, bisa tuhumarsu da yaɗawa gami da ɗaga tutocin Rasha a Kano, yayin zanga-zangar da dubban matasa suka gudanar kan tsadar rayuwa a faɗin ƙasar, da ta kai ga salwantar rayukan mutanen da kungiyar Amnesty ta ce adadinsu ya kai 20. Sanarwa daga rudunar tsaron Najeriya na bayyana cewa,kafin kamen dai, sai da jami’an tsaron Najeriyar suka cafke aƙalla mutane 30 saboda ɗaga tutocin Rasha da suka riƙa yi yayin zanga-zangar ta gama-gari, a wasu jihohin ƙasar ciki har da Kano.Kan haka Aisha Shehu Kabara ta tattauna da kakakin rundunar ‘Yan Sandan jihar Kano SP Abdull Haruna Kiyawa, wanda yayi ƙarin hake kan halin da ake ciki.

página 2 de 2