Informações:
Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Halin da masana'antun arewacin Najeriya ke ciki na rashin wutan lantarki
31/10/2024 Duración: 03minMasu masana'antu a arewacin Najeriya sun bi sahun sauran jama'ar yankin wajen bayyana damuwarsu a kan halin da suka samu kansu na rashin wutan lantarki sama da kwanaki goma. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mataimakin shugaban ƙungiyar masu masana'antu ta ƙasa MAN, Ali Safiyanu Madugu.
-
Farfesa Shehu Abdullahi Zuru game da binciken wasu alkalai a jihar Rivers
30/10/2024 Duración: 03minBabbar mai shari'a a Najeriya tare da Hukumar Kula da Ayyukan Shari'a ta NJC sun kaddamar da bincike a kan yadda wasu alkalai a jihar Rivers suka dinga bada hukunce hukunce da ke karo da juna dangane da zaben kananan hukumomin da aka yi a jihar. Wannan umarni na zuwa ne bayan an samu irin wannan matsala a jihar Kano. Saboda haka Bashir Ibrahim Idris ya tintibe masanin ɓangaren shari'a Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na jami'ar Baze dake Abuja. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.........
-
Murtala Aliyu kan matsayar ACF na rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya
29/10/2024 Duración: 03minƘungiyar Tintiba ta Arewacin Najeriya da ake kira ACF, ta bi sahun wasu jama'ar yankin wajen bayyana damuwarta kan matsalar rashin wutar da ake fuskanta na sama da mako guda a yankin, inda ta buƙaci shugaban ƙasar da ya kafa dokar ta ɓaci a kan lamarin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren kungiyar, Malam Murtala Aliyu, wanda tsohon ministan wutar lantarki ne a ƙasar Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana........
-
Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina kan rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya
28/10/2024 Duración: 03minMazauna yankin Arewacin Najeriya sun kwashe kwanaki 7 ba tare da hasken wutar lantarki ba, abinda ya yi sanadiyar durkushewar jama'a musamman masu sana'oin da suka dogara ga wutar. Wannan matsala na barazana ga rayuwa da kuma tattalin arzikin yankin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daya daga cikin dattawan yankin, Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu ta su........
-
Dokta Abbati Baƙo kan taron BRICS da ake yi a Rasha
24/10/2024 Duración: 03minShugaban Rasha Vladimir Putin ya ce taron kasashen BRICS dake gudana a kasarsa zai duba yiwuwar samar da wata sabuwar tafiya wadda za ta yi gogaggaya da wadda ake amfani da ita a duniya yanzu haka.Akalla shugabannin kasashe 30 ke halartar taron a birnin Kazan.Domin tasirin wannan kungiya ta BRICS dake Shirin kawo sauyi a duniya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Bako masanin siyasar duniya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Dr Yahuza Ahmad Getso kan fargabar kwararar ƴan ta'adda zuwa jihar Kano
22/10/2024 Duración: 03minWani sabon rahoton binciken kwakwaf da aka gudanar ya bankado yadda ‘yan ta’adda daga jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina da kuma Kaduna ke tsallakawa jihar Kano domin samun mafaka. Jihar Kano ce dai ke da dama-dama ta fannin ingancin tsaro a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.Shin yaya masana ke kallon wannan sabon salo da kuma hatsarin da yake da shi, Rukayya Abba Kabara ta tattauna da Dr Yahuza Ahmad Getso masanin tsrao a Najeriya, ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar......
-
Dr Kasum Garba Kurfi game da yabawa tsarin tattalin arzkin Najeriya da bankin duniya yayi
21/10/2024 Duración: 03minBankin duniya ya yaba da sauye sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa, tare da bai wa hukumomin ƙasar shawarar kar su kuskura su koma da baya. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da talakawan ƙasar ke kokawa saboda ƙuncin rayuwa. Dangane da wannan matsayi Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Kasum Garba Kurfi. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu..............
-
Sojojin Nijar sun gaza a yaƙi da rashawa - Transparency International
18/10/2024 Duración: 03minƘungiyar Transparency International da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, reshen Jamhuriyar Nijar ta fitar da wani sabon rahotoda ke zargin sojojin ƙasar da gazawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma hana fararen hula guraben shugabancin hukumomin gwamnati. Dangane da wannan zargi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban Transparency International, reshan Nijar, Mamman Wada.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Kaften Isa Usman: Halin da shugaba Paul Biya na Kamaru ke ciki
11/10/2024 Duración: 03minYayin da tababa da rashin tabbas suka mamaye halin da shuhgaban Kamaru Paul Biya ke ciki, gwamnatin ƙasar ta haramta wa kafofin yaɗa labarai sharhi dangane da shugaban. A kan wannan batu ne, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kaften Isa Usman, tsohon dogarin Ahmadou Ahidjou da kuma shi kansa Paul Biya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Comrade Umar Danjani Hadejiya kan ƙara kuɗin man fetur a Najeriya
10/10/2024 Duración: 03minA karo na 4 tun bayan hawa karagar mulkin shugabancin Najeriya da Bola Ahmed Tinubu yayi, kamfanin man NNPCL ke sanar da ƙara farashin man fetur, inda yanzu farashin ya koma naira 998 a Lagos, ya yin da Abuja kuma ya koma naira dubu 1 da naira 30. Wannan ya sa talakawan ƙasar sake gabatar da korafinsu saboda yadda farashin zai sake shafar kayan masarufi. Dangane da wannan sake karin, Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da Comrade Umar Danjani Hadejiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu......
-
Prof Shehu Abdullahi Zuru kan binciken yadda ƴan Afrika basa jin daɗin mulkin dimukaradiya
09/10/2024 Duración: 03minShugaban Gidauniyar Shehu Musa Yar Adua Akin Kekere-Ekun, ya bayyana cewar kashi 80 na jama'ar nahiyar Afirka ba sa jin daɗin yadda zaɓaɓɓun shugabanninsu ke tafiyar da mulkin dimukiraɗiya a ƙasashen su. Jami'in ya ce akwai wagegen giɓi tsakanin yadda shugabannin ke mulki da kuma buƙatun jama'a, musamman abinda ya shafi ayyukan da suke so. Dangane da binciken da Gidauniyar ta yi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze da ke Abuja. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Sama'ila Mohammed kan ɗauki-ɗora a zaɓen ƙananan hukumomi a Najeriya
08/10/2024 Duración: 03minGa alama yunkurin tabbatar da dimokiradiya a yankunan kananan hukumomin Najeriya da kuma sake musu mara domin cin gashin kansu na ci gaba da fuskantar kalubale, ganin yadda zabukan kananan hukumomi suka zama dauki dora, inda jam'iyyar gwamnan da ke mulkin jiha ke lashe daukacin kujerun kananan hukumomin jihar. Domin sanin inda matsalar ta ke da illar da za ta yi wa dimokiradiya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Samaila Muhammed, tsohon shugaban karamar hukumar Jos dake Jihar Filato, kuma tsohon dan majalisar tarraya. Ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Dr Elharun Muhammed kan cika shekara ɗaya da faro yakin Hamas da Isra'ila
07/10/2024 Duración: 03minYau ake cika shekara guda da kazamin harin da mayakan Hamas suka kai wa Isra'ila wanda ya yi sanadiyar barkewan yakin da ya lakume rayukan mutane sama da dubu 45 daga bangarorin biyu. Duk wani ƙoƙarin sasanta rikicin ya gagara, yayin da yakin ke ci gaba da fadada. Dangane da halin da ake ciki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Elharun Muhammed, mai Cibiyar kula da manufofin ƙasashe da kuma ci gabansu. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.......
-
Isra'ila ta sha alwashin daukar fansa a kan Iran, ya yin da Iran ta ce za ta mayar da martani mai karfi
04/10/2024 Duración: 03minKasar Israila ta sha alwashin daukar fansa dangane da hare haren da Iran ta kai cikin kasar ta, ya yin da Iran ke cewa duk lokacin da aka kai mata hari za ta mayar da martani mai karfi. Tuni wannan mataki ya dada jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin tashin hankali. Dangane da halin da ake ciki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon jakadan Najeriya a Iran, Ambasada Abubakar Chika, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana
-
Hare haren Iran a kan Isra'ila ya dada fadada yakin dake gudana a Gabas ta Tsakiya- Dr Abbati
03/10/2024 Duración: 03minHare haren da kasar Iran ta kaddamar a kan Isra'ila ya dada fadada yakin dake gudana a Gabas ta Tsakiya, tun bayan kazamin harin da mayakan Hamas suka kaddamar a kan yahudawa ranar 7 ga watan Oktobar bara.Martanin da Isra'ila ta mayar ya yi sanadiyar kai hare hare a yankunan Falasdinawa da Yemen,Lebanon,Syria da kuma Iran abinda ya yi sanadiyar hallaka mutane sama da dubu 40.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Bako, mai sharhi a kan siyasar duniya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana
-
Shugaban matasa Muntaqa Abdulhadi Dabo kan taron matasan da Tinubu zai shirya
02/10/2024 Duración: 03minShugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin gudanar da wani taron matasa na kasa domin basu damar tattauna matsalolin da suka addabe su da zummar share musu hawaye. Ana saran wannan mataki ya kwantar da hankalin fusatattun matasan wadanda ke korafi a kan yadda ake gudanar da mulkin Najeriya.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Muntaqa Abdulhadi Dabo, daya daga cikin fitattun matasan kasar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Sanata Mamman Abubakar Danmusa kan samun ƴancin kan Najeriya
01/10/2024 Duración: 03minYau Najeriya ke cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga Turawan Ingila, inda 'yan kasar ke tilawar irin ci gaban da aka samu da kuma matsalolin da aka fuskanta a kokarin ganin ci gabar kasar. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daya daga cikin 'yan mazan jiya, wadanda suka ga gwagwarmayar neman 'yancin, kan asuka taka rawa a bangaren jagorancinta, wato Sanata Mamman Abubakar Danmusa, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Jamhuriya ta 2. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.......
-
Ibrahim Garba Wala game da halin da ake ciki na bada agaji a Maiduguri
30/09/2024 Duración: 03minAkalla makwanni 3 bayan ambaliyar da ta yiwa mazauna birnin Maiduguri illa, har yanzu wasu daga cikin wadanda ibtila'in ta ritsa da su na cikin mawuyacin hali, ya yin da ake ci gaba da gudanar da aikin jinkai. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ibrahim Garba Wala, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin da ke aikin taimakawa wadanda hadarin ya ritsa da su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar ta su......
-
Yusuf Tuggar a kan Najeriya da kujerar dindindin a kwamitin Tsaro MDD
27/09/2024 Duración: 03minKamar yadda wata kila kuka ji a cikin labaran duniya, Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambassada Yusuf Tuggar ya bayyana manyan dalilan da ya kamata a yi dubi da su domin sanya kasar a matsayin mambar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban Sashen Hausa na RFI, Mr Joseph Penney ya tattauna da ministan a zauren Majalisar dake ci gaba da gudanar da taronta a New York ta kasar Amurka, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Hukumar GIABA ta shirya taron fadakar da 'yan kasuwa da masu masana'antu da kuma lauyoyi
26/09/2024 Duración: 03minHukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasashen Afirka ta Yamma, wato GIABA ta shirya wani taron fadakar da 'yan kasuwa da masu masana'antu da kuma lauyoyi a kan hakkin da ya rataya a kansu na kin bada dama ga masu halarta kudaden haramun ko kuma 'yan ta'adad su yi amfani da su wajen boye kudaden sata. Taron na kwanaki 2 na gudana ne a birnin Lagos. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai magana da yawun GIABA Mr Timothy Melaye, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.