Ilimi Hasken Rayuwa

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:58:14
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episodios

  • Har yanzu tsarin jagoranci da bada shawarwari na tasiri a makarantu?

    27/08/2024 Duración: 09min

    Shirin a wannan mako ya duba yadda tsarin jagoranci da bada shawarwari a makarantu, tsarin da ke taimakawa dalibai zabar irin fannin da suke son kwarewa akai, inda sun kai matakin jami'a da sauransu. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara

  • Tsarin ilimin Sakandire kyauta a Ghana ya ƙarfafa gwiwar dubban ɗalibai

    20/08/2024 Duración: 09min

    Shirin ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon ya mayar da hankali kan tsarin bayar da ilimin Sakandiren kyauta a Ghana, wanda ya taimaka matuka wajen ƙara yawan Ɗaliban da ke halarta karatu a wannan mataki. Duk da cewa shirin ya laƙume kuɗaɗe masu tarin yawa amma gwamnatin ƙasar ta Ghana ta ce ko shakka babu kwalliya ta biya kuɗin sabulu cikin shekaru 5 da fara tsarin.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shiri.

  • Yadda tsarin koyo da koyarwa a karni na 21 ke saukakawa wurin fahimtar karatu

    30/07/2024 Duración: 09min

    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimtar da ɗalibai, sannan ɗalibai su ma su ji sauƙin fahimtar abin da ake koyar da su a aji. A wannan mako, mun dubi yadda tsarin yake aiki tare yadda ya sauƙaƙa wa malamai da ɗalibai wurin fahimtar karatu a wannan zamani musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

  • Karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana

    23/07/2024 Duración: 09min

    Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.

  • Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya

    16/07/2024 Duración: 10min

    A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami’o’in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.Shugabannin Jami’o’in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...

  • Dalilan mummunar faduwar jarabawa da daliban jamhuriyar Nijar suka yi a bana

    09/07/2024 Duración: 09min

    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda dalibai a jamhuriyar Nijar suka yi mummunar faduwa a sakamakon jarabawar karshe ta makarantar Sakandare. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadir Haladu kiyawa

  • Yadda ayyukan ƴan ta'adda suka kassara harkokin Ilimi a Arewacin Najeriya

    02/07/2024 Duración: 09min

    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta’adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar. Bincike ya nuna cewa, tun bayan harin na 2014, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai makamancinsa a kimanin makarantu 17, waɗanda suka haɗa da makarantun Firamare da sakandare da ma manyan makarantun gaba da sakandare, inda suka yi garkuwa da dalibai da dama, an sako wasu bayan biyan kuɗin fansa, wasu kuwa suna rike a hannunsu  har zuwa yanzu. Cikin shekaru goma da fara ƙaddamar da irin wannan ta'addanci kan makarantu da ɗalibai, masana sun bayyana shakku kan gwamnatin Najeriya tare da zarginta da nuna halin ko in kula kan ilimi tare da rayukan al'ummar kasar musamman ɗalibai. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...

  • Tasirin sabuwar hanyar koyarwa a duniya

    25/06/2024 Duración: 09min

    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance. Ita dai sabuwar hanyar koyarwa wato Innovative Teaching Method, hanya ce da ta sha bambam da hanyoyin koyarwa da aka saba gani a lokutan baya, domin ita ana koyar da ɗalibai ne bisa doron buƙatarsu ta koyo, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da kuma na’urori, batare da malami ya zama shi ne ruwa kuma shi ne langa ba.

  • Yadda jaddawalin karatun Najeriya ke haifar ga koma-baya a Fannin Ilimin Kasar

    18/06/2024 Duración: 09min

    A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne a kan yadda tsarin jaddawalin karatun Najeriya ke haifar da koma-baya a fannin ilimin kasar. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...

  • Ban-bancin da ke da shi wajen karatun Ilimin kimiyya da fasaha a kasashen Duniya

    11/06/2024 Duración: 09min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha tsantsa hadi da lissafi, wato STEM Education a turance. Mafi yawancin kasashen Duniya da suka ci gaba, na bawa wannan tsari na Ilimin Kimiyya da fasaha tsantsa hadi da Lissafi fifiko a makarantunsu, la’akhari da yadda kimiyya da fasaha a wannan zamani suka zama ginshinkin ci gaba a sararin wannan duniyar. Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

  • Jami'ar Umaru Musa ta yaye sama da dalibai dubu goma a wannan shekarar

    04/06/2024 Duración: 10min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake ci gaba da samun ci gaba a bangaren daliban da ke zuwa makaranta a yankin Arewacin Najeriya. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a da ke jihar Katsina ta samu nasarar yaye sama da dalibai dubu 10 a wannan shekarar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin ta re da Abdulkadir Haladu Kiyawa........

  • Yadda Jami'o'in Najeriya suka fara mayar da hankali kan karatun koyon sana'a

    21/05/2024 Duración: 09min

    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda aka fara mayar dahankali a kan karatun koyon sana'a a Kwalejoji da Jami'o'i a Najeriya.Kuna iya Latsa alamar sauti domin sauraron shirin...

  • Yadda Dalibai ke bada gudunmawa wajen sarrafa sinadaran da basa gurbata muhalli

    14/05/2024 Duración: 10min

    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda Dalibai a kasashen da suka ci gaba ke bayar da gudunmawa wajen sarrafa sinadarin "Hydrogene" da baya gurbata muhalli sosai, ta fuska kere-kere da nufin inganta iskar da ake shaka, bisa tallafin gwamnatocin kasashensu.

  • Yadda matasa ke dukufa wajen amfani da Internet don dogaro da kai

    07/05/2024 Duración: 10min

    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako zai duba yadda matasa suka dukufa wajen amfani da yanar gizo don dogaro da kai. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

  • Karuwar masu mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya, na barazana ga karewar kwararru

    26/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama. Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu.Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

  • An samar da cibiyar sadarwa a jahar Bauchi don saukakawa dalibai wajen bincike

    19/03/2024 Duración: 09min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama’are ke cikin wannan rukuni. Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

  • Taro kan gudummawar kafafen yada labarai a bangaren tsaro a jami'ar ABU Zaria

    05/03/2024 Duración: 09min

    Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya  sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Ya yi wannan ne da zummar taimaka wa kokarin da al'umma ke yi wajen warware wa kansu matsalar tsaron da ke damun su.

  • Yadda dalibai ke barin karatu a Nijar don tafiya neman kudi a wasu kasashe

    27/02/2024 Duración: 10min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi. A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami’a.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

  • Yadda gwamnatin jahar Neja ta fara horas da dalibai sana'oin dogaro da kai

    20/02/2024 Duración: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

  • Yadda amfani da komfuta ya shafi kyaun rubutun dalibai

    31/01/2024 Duración: 09min

    A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau’I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya.Tun bayan samar ko kuma kirkirar na’urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama’a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita. 

página 1 de 2