Sinopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodios
-
Dalilan da ya sa masana ke neman a yi taka tsan-tsan wajen amfani da fasahar AI
10/06/2025 Duración: 09minShirin Ilimi na wannan mako ya yi duba ne kan muhawarar da ake ci gaba da tafkawa kan fasahar nan ta kimsawa na’ura irin basirar ɗan Adam wadda aka sani da AI, wasu masana dai na cigaba da gargaɗin cewa ya zama dole a yi taka tsan-tsan domin bai kamata a saki jiki da wannan Fasaha ta AI ba, duk da amfanin da ta ke tattare da ita wajen sauƙaƙa ayyuka masu wahala da ɗan Adam ke yi. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna.................
-
Yadda faɗuwar jarabar JAMB ta shafi ɗalibai da ke neman gurbin ƙaratu a Najeriya
03/06/2025 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar da aka samu ta faɗuwar jarabar sharar fage ta shiga jami'o'in Najeriya JAMB, da hukumar shirya jarabawar ta ce hakan ya faru ne a sakamakon tangarɗar da aka samu ta na'ura a lokacin rubutawa. Matslar da ta hana shafi ɗalibai dubu 300 da suka rubuta jarabawar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.........
-
Yadda Malaman makarantu suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Abujan Najeriya
27/05/2025 Duración: 09minShirin na wannan mako ya ba da hankali ne kan bikin ranar yara ta duniya wanda aka saba gudanarwa a ranar 27 ga watan mayun kowacce shekara, a Najeriya yayin da ake bikin wannan rana Malaman Makarantun firamare a Abuja babban birnin ƙasar ne ke shiga watanni na uku da fara yajin aikin sai Baba ta gani, sakamakon rashin fara aiwatar da sabin tsarin mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 kamar yadda ƙungiyarsu ta Malaman makarantu ta bayyana. lamarin da ya ta da yajin aikin gargaɗi a baya kafin su tsunduma cikin wanda suke kai a yanzu.
-
Yadda satar amsa tsakanin dalibai ke yiwa ilimi illa musamman a Najeriya
20/05/2025 Duración: 09minShirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali kan Illonlin satar amsa tsakanin Dalibai a yayin rubuta jarabawa. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna