Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:55:52
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodios

  • Ra'ayoyin masu saurare kan matakin IPOB na shiga tattaunawa da Najeriya

    20/06/2024 Duración: 10min

    Jagoran IPOB da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu, ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawa da gwamnati domin kawo ƙarshen kai-da-kawon da ake yi da shi a gaban kotu. Kanu, wanda mahukuntan ƙasar Kenya suka kama tare da miƙa wa Najeriya shi tun a 2021, yanzu haka yana fuskantar tuhume-tuhume ciki har da na ta’addanci da kuma cin amanar ƙasar.Shin ko tattaunawa ita ce mafita don warware wannan al’amari?Ko wataƙila sakin Nnamdi Kanu zai iya taimakawa domin samar da zaman lafiya musamman a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Ayeeshat Jibrin Ahmed

  • Ra'ayoyi kan rikici tsakanin Nijar da Benin

    19/06/2024 Duración: 10min

    Rikici tsakanin Nijar da Jamhuriyar Benin, ga alama zai iya ɗaukar dogon lokaci kafin a iya warware shi, saboda ko bayan rufe iyaka, Nijar ta rufe bututun da ke isar da ɗanyan mai zuwa Cotonou. Wani abu da ya ƙara zafafa wannan rikici shi ne, kama wakilan da Nijar ta tura don sanya ido game da yadda ake fitar da man, inda aka yanke musu hukuncin daurin talata na watanni 18 a kasar ta Benin.Anya akwai alamun ƙasashen biyu za su sulhunta wannan rikici da ke tsakaninsu?Wane tasiri ku ke ganin cewa wannan rikici wajen hana cuɗanya ta tattalin arziki a tsakanin wadannan ƙasashe?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin

  • Ra'ayoyi kan samar wa da Afrika alluran rigakafin cututtuka

    18/06/2024 Duración: 10min

    Gabanin taron da za a gudanar ranar Alhamis a birnin Paris don taimaka wa Afirka dangane da yadda za ta samar wa kanta da alluran rigakafin kariya daga wasu cututuka a wadace, tuni aka samu alƙawurran sama da Euro biliyan ɗaya daga ƙasashe da da kuma ƙungiyoyi daban daban a cewar fadar gwamnatin Faransa. Wadannan kuɗade za a yi amfani da su ne don tabbatar da cewa kamfanonin sarrafa magunguna sun samar da alluran rigakafin cututuka kamar Korona, Cholera da kuma zazzaɓin cizon sauro a cikin nahiyar.Shin me za ku ce a game da wannan tallafi na ƙasashen duniya zuwa ga nahiryar Afirka?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin

  • Ra'ayoyin Masu Saurare kan farashin raguna

    13/06/2024 Duración: 09min

    Yayin da ya rage kwanaki kaɗan a gudanar da Sallar Idil-kabir wato sallar layya, yanzu haha hankulan mafi yawan jama’a sun karkata zuwa ga batun sayen ragunan layya.Yaya farashin raguna da kuma sauran dabbobin da ake layya da su a kasashenku?Shin ko yanayin da ku ke ciki a yau, zai ba ku damar yanka dabbar layya a wannan shekara? Wannan shi ne abin da shirin ya tattauna a kai.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

página 2 de 2