Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Ra'ayoyin masu saurare kan zanga-zangar 'yansanda a Najeriya
22/07/2025 Duración: 09minA babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, ɗaruruwan ƴansanda da suka yi ritaya kuma bisa ga dukkan alamu da yawun waɗanda suke bakin aiki a yanzu ne suka gudanar da zanga-zangar neman a cire su daga tsarin fanshon adashen gata, wanda suka ce babu abin da ya yi face jefa su cikin baƙin talauci bayan shafe shekaru suna wa ƙasar hidima. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi....
-
Yadda Isra'ila ke kashe Falasɗinawa masu jiran tallafin abinci
21/07/2025 Duración: 09minShirin ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda Isra'ila ta mayar da guraren rabon abincin tallafi a Gaza tarkon mutuwa. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan rashin yiwa yara rigakafin cutuka a Najeriya a 2024
16/07/2025 Duración: 09minWani sabon rahoton Asusun kula da ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ƙananan yara sama da miliyan 14 ne a fadin duniya ba su samu alluran rigakafin cutukkan da ke addabar yara a shekarar 2024 ba, kuma sama da miliyan biyu daga cikin wannan adadi a Najeriya suke. Rashin wannan rigakafi na iya jefa waɗannan yara cikin hatsarin kamuwa da cutukan da ake iya samun kariya daga gare su. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Shugaban Kamaru Paul Biya zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar karo na 8
15/07/2025 Duración: 09minShugaban Kamaru Paul Biya ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a karo na 8 yana mai shekaru 92 da haihuwa, inda ya yi iƙirarin cewa matasa da mata ne zai fi bai wa fifiko idan ya samu ya zarce. Wani saƙo da Biya mai shekaru 92 ya wallafa a shafinsa na Twitter ne ke sanar da wannan mataki wanda ya kawar da jita-jitar da ke nuna cewa shugaban a wannan karon bashi da sha'awar tsayawa takara don neman wa'adi na gaba. Fiye da shekaru 40 kenan Paul Biya ke jagorancin Kamaru kasancewarsa shugaba na biyu da ya jagoranci ƙasar tun bayan samun ƴancinta daga Faransa wato bayan murabus ɗin shugaba Amadou Ahidjo. Idan har Paul Biya ya yi nasarar lashe zaɓen da zai bashi damar sake yin shekaru 7 a karagar mulki, kenan shugaban mafi daɗewa kan mulki, zai tasamma shekaru 100 na rayuwarsa a karagar mulki karon farko da ake ganin irin hakan a tarihi. Shiga alamar sauti, domin sauraro cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan mutanen da 'yanbindiga suka kashe a cikin watanni 6
09/07/2025 Duración: 10minA Najeriya, wasu alƙaluman hukumar kare hakkin ɗan adam ta ƙasar sun ce adadin mutanen da ƴanbindiga suka kashe a cikin watanni shida na farkon wannan shekarar ya zarce na ilahirin shekarar da ta gabata, inda a watan da ya gabata kawai mutane 606 ne masu ɗauke da makamai suka halaka. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan yadda ambaliya ke yin ɓarna a wasu biranen Afrika
07/07/2025 Duración: 10minAmbaliyar ruwa na ci gaba da yin ɓarna a wasu biranen ƙasashen Afrika, inda ko a baya-bayan nan ta laƙume rayuka fiye da 600 a ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar Nejan Najeriya yayin da tituna suka fara cika da ruwa a wasu ƙananan hukumomin jihar Kano, baya ga babban birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar da aka samu iftila’in ambaliyar a kwanakin baya. Ya ya matsalar ta ke a yankunan ku, ko wani mataki kuke ɗauka don ganin kun kare kanku daga iftila’in ambaliyar ruwan yayin da daminar bana ta sauka? Shin ko akwai wasu matakai da gwamnatocinku ke ɗauka?
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
04/07/2025 Duración: 10minA duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Yadda wasu fitattun ƴansiyasa a Najeriya suka kafa wani sabon ƙawance
03/07/2025 Duración: 10minWasu fitattun ƴansiyasa a Najeriya, sun sanar da kafa wani sabon ƙawance da zummar ƙwace mulki daga hannu shugaba Bola Tinubu a shekara ta 2027. To sai dai abin lura a nan shi ne, waɗanda suka ƙulla ƙawancen mutane ne da suka taɓa riƙe muhimman muƙamai ƙarƙashin gwamnatoci daban-daban ciki har da ta APC. Abin tambayar shine, ko waɗanne irin alƙawura ne da za su sake gabatar wa 'yan ƙasar domin samun ƙuri’aunsu? Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kashe 'yan ta'adda da jami'ai su ka yi a Najeriya
02/07/2025 Duración: 10minA Najeriya, ga alama sabon salon da hukumomin tsaro na tarayya da kuma na jihar Zamfara su ɓullo da su, sun fara yin tarisi a yaki da ayyukan ƴanbindiga da suka addabi jama’ar yankin. Bayanai sun ce farmakin da ƴan sa-kai suka kai ƙarshen makon jiya, ya yi sanadiyyar mutuwar ƴanbidigar kusan 200 ciki har da manyan kwamandojin Bello Turji. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin jama'a mabanbanta...
-
Kan tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila
25/06/2025 Duración: 09minShirin na yau ya baku damar tofa albarkacin bakinku game da tsagita wuta da aka yi tsakanin Iran da Isra'ila bayan kwashe kusan kwanaki 12 ana gwabza yaƙi. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
-
Ra'ayoyin masu sauraron kan shawarar gina katanga kan iyakokin Najeriya
05/06/2025 Duración: 10minBabban hafsan sojojin Najeriya ya bayar da shawarar gina katanga kan iyakokin ƙasar da maƙotanta don magance matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da su. Janar Christopher Musa ya bayar da misali da ƙasashen Pakistan da kuma Saudiyya, waɗanda ya ce sun gina irin wannan katanga tsakaninsu da maƙota saboda dalilai na tsaro.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin jama'a kan Gasar Zakarun Turai ta bana da PSG ta lashe
03/06/2025 Duración: 08minKaron farko a tarihi, ƙungiyar Paris Saint Germain ta Farnasa ta yi nasarar lashe kofin gasar Zakarun Turai ta wannan kaka bayan da ta doke Inter Milan ta Italiya, inda ta zama ta biyu da ta taɓa cin wannan kofidaga Faransa. Wani abin lura a game da wannan wasa, shi yadda PSG ta lallasa abokiyar karawarta da ci 5 da banza.Me za ku ce a game da wannan nasara da PSG ta samu?Ko meye ra’ayoyinku a game da yadda gasar ta Zakarun Turai ta wannan kaka ta gudana?
-
Ra'ayoyin masu saurare kan bikin cika shekara 53 da haɗewar Kamaru
20/05/2025 Duración: 10minA wannan talata, al’ummar Kamaru na bikin cika shekaru 53 da haɗewar yankunan da ke amfani da Faransanci da masu amfani da harshen Ingilishi, waɗanda kafin nan suna zaune da juna ne a ƙarƙashin tsarin tarayya. To sai dai a daidai yayin da ake wannan biki, yanzu haka akwai masu gwagwarmaya da makamai don samar wa yankunan da ke turancin Ingilishi ƴanci.Shin ko me za ku ce a game da wannan haɗewa?Ko waɗanne matakai ku ke ganin cewa sun dace a ɗauka domin dawo da yarda a tsakanin bangarorin biyu?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ra'ayoyi kan matakin Ghana na kama masu bace-barace
19/05/2025 Duración: 10minMatsalar barace-barace a kan titunan manyan birane a Yammavin Afirka sai daɗa yin ƙamari take, to sai dai bisa ga dukan alamu mahukunta a ƙasar Ghana sun ƙuduri aniyar kawo ƙarshen wannan ɗabi’a. Domin a cikin makon jiya, jami’an tsaro sun cafke mabarata sama da dubu biyu a birnin Accra kawai, kuma yawancinsu ƴan asalin ƙasashen Najeriya, Nijar, Burkina Faso da Mali ne.Shin ko akwai dalilan da za su sa jama’a su mayar da bara a matsayin sana’a?Ko waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin kawo ƙarshen wannan ɗabi’a ta bara?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
16/05/2025 Duración: 10minA duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan matakin Nijar na hana fitar da dabbobi zuwa ƙetare
15/05/2025 Duración: 10minMakonni kaɗan gabanin bukukuwan Sallar Layyah, mahukuntan jamhuriyar Nijar sun bayar da umurnin hana fitar da dabbobi zuwa ƙetare. Ga alama dai an ɗauki matakin ne don hana tashin farashin dabbobi a wannan lokaci, yayin da wasu ke cewa matakin zai iya cutar da tattalin arzikin ƙasar.Abin tambayar shine, menene amfani ko kuma illar wannan mataki ga ƙasar?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan yadda ƴanbindiga suka tsananta kai hare-hare
14/05/2025 Duración: 09minHare-haren ƴanbindiga na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Najeriya, inda a baya-bayan nan suka tsananta kai farmaki hatta akan sansanonin soji, kusan a iya cewa haka take a sauran yankin sahel musamman Burkina Faso, lamarin da kanyi sanadin mutuwar jami’an tsaro masu tarin yawa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a kan wannan maudu'in.......
-
Ra'ayoyi kan kula da lafiyar kwakwaluwa
13/05/2025 Duración: 10minShin ko kun san muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa kuwa? Wannan tambaya ce mai matuƙar muhimmanci, lura da cewa yanzu haka akwai ɗimɓin mutane da ke fama da wannan matsala a sassan duniya. Yayin da wasu ke kira wannan lalura a matsayin hauka, masana kuwa na cewa hatta shiga yanayi na damuwa ko da ƙuncin rayuwa na iya haddasa wannan matsalar.Shin ko wace irin kulawa ku ke bai wa lafiyar ƙwaƙwalwa?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
09/05/2025 Duración: 10minA duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan ficewar Meta daga Najeriya
05/05/2025 Duración: 09minKamfanin Meta da ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya yi barazanar ficewa daga Najeriya bayan da aka lafta masa biyan tarar dala miliyan 290 saboda karya ƙa’ida. To sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ko da kamfanin ya janeye daga ƙasar, to dole ne sai ya biya wannan tarar. Za mu so jin ra’ayoyinku a game da wannan takun-saka tsakanin Najeriya da kuma wannan shahrarran kamfani na sadarwa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.