Taa Ka Lashe | Deutsche Welle

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 16:37:31
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.

Episodios

  • Taba Ka Lashe: 08.06.2022

    14/06/2022 Duración: 09min

    Shirin ya yi nazari kan yadda mutane musamman a kasar Hausa, ke yin adashi domin taimakon kansu.

  • Taba Ka Lashe (25+26.05.2022)

    31/05/2022 Duración: 09min

    Kungiyar DRPC na daga cikin kungiyoyi a jihar Jigawa da ke fadi-tashi wajen ganin sun ciyar da fannin ilimi gaba a Najeriya.

  • Taba Ka Lashe (18.05.2022)

    24/05/2022 Duración: 09min

    Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya garzaya jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda ya yi nazari kan al'adar maita.

  • Taba Ka Lashe: Sallah a masarautar Abzin

    10/05/2022 Duración: 09min

    Saurari yadda aka gudanar da bikin Sallah karama a fadar sarkin Abzin na jihar Agadez. An shafe kwanaki uku ana bukukuwan al’adar da ke kayatar da jama’a.

  • Taba Ka Lashe: Batun amfani da harshen gida a Jamhuriyar Nijar

    12/04/2022 Duración: 09min

    Shirin ya yada zango a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar inda muka duba batun yadda iyaye ke sakaci wajen koyar da yara harshen gida.

  • Taba Ka Lashe 16.03.2022

    22/03/2022 Duración: 09min

    Al'adar bikin aure a kasar Guddirawa da ke jihar Bauchin Najeriya mai dumbin tarihi.

  • Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri

    15/03/2022 Duración: 09min

    Aure na daya daga cikin al'adun da Guddurawa suke masa hidima ta gani a fada fiye da duk wata al'adar su, kama daga farkon nema tsakanin saurayi da budurwa har zuwa lokacin bayarwa da mai gaba daya lokacin bikin auren. Kuma har zuwa yanzu guddurawa ba su bari ba. Wannan shi ne batun a shrin Taba Ka ashe na wannan mako ya yi duba a kai. Daga kasa za a iya sauraon sauti

  • Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri

    15/03/2022 Duración: 09min

    Al'adar bikin aure a Guddiri a Jihar Bauchi dadaddiyar masarauta ce mai dumbin tarihi, kuma guddurawa suna da wasu fitattun al'adunsu da suka banbanta su da sauran masarautun Bauchi.

  • Taba Ka Lashe: 02.03.2022

    08/03/2022 Duración: 09min

    Ko har yanzu ana amfani da wakokin gargajiya da kayan kidan harshen Hausa a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: Rayuwar Musulmi da Kirista

    15/02/2022 Duración: 09min

    Musulmi da Kirista a Jihar Filaton Najeriya na zaune a unguwani dabam-dabam sabanin yadda a baya al'ummomin biyu ke zaune wuri guda suna cudanya.

  • Taba Ka Lashe 02.01.2022

    08/02/2022 Duración: 09min

    Shirin na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan kirari. Ya al'adar kirari take a kasashen Afirka?

  • Taba Ka Lashe: 26.01.2022

    01/02/2022 Duración: 09min

    Shirin na wannan lokaci ya ziyarci jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, inda ya gano wani Masallaci da ya kwashe shekaru aru-aru.

  • Taba Ka Lashe: 29.12.2021

    04/01/2022 Duración: 09min

    Ko kun san su wanene mafarauta da 'yan tauri da kuma yadda suke samun taurin? Ku saurari Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: 22.12.2021

    28/12/2021 Duración: 10min

    Shirin ya duba yunkurin farfardo da wata sarautar gargajiya ta kabilar Abzinawa a garin Afess na jahar Agadez a Nijar.

  • Taba Ka Lashe: 15.12.2021

    21/12/2021 Duración: 09min

    An gudanar da bikin nadin sababbin sarautu, a masarautar Hausawan Turai. Karin bayani cikin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: 08.11.2021

    14/12/2021 Duración: 09min

    Mata na taka muhimmiyar rawa, wajen magance rikice-rikicen kabilanci da na addinai da makamantansu. Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: 24.11.2021

    30/11/2021 Duración: 09min

    Ko kun san yadda mabiya darikun Sufaye ke ziyara Kushewar Waliyai a Maroko? Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe

    16/11/2021 Duración: 09min

    Wurin da ake tsugune da daruruwan mata da ake zargi da aikata maita a wata cibiya ta musamman da ake wa lakabi da "Sansanin mayu” a arewacin Ghana.

  • Taba Ka Lashe: 27.10.2021

    02/11/2021 Duración: 09min

    A duk ranakun 12 ga watan Rabi'ul Auwal na ko wacce shekara, al'ummar Musulmi a fadin duniya kan yi bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). A wannan shirin mun yi nazarin yadda aka gudanar da bukukuwan na bana a jihar Kano da ke Najeriya.

  • Taba Ka Lashe 22.09.2021

    28/09/2021 Duración: 09min

    Yadda zamani ke shirin gusar da al'adun gargajiyan jahar Gaya a jamhuriyar Nijar. Latsa kasa don jin cikakken shirin.

página 4 de 5