Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan ingancin dimokuraɗiyya a Najeriya
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:09:27
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
A Najeriya, yanzu haka wasu sun fara nuna fargaba a game da yadda tsarin dimokuradiyya ke gudana a kasar, musamman lura da yadda da zarar aka gudanar da zaben kananan hukumomi, to ko shakka babu jam’iyyar da ke rike da kujerar gwamna ce za ta lashe zaben babu tantama. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka bai wa kananan hukumomin damar cin gashin kansu.Abin tambaya anan shi ne, me ya sa a kullum jam’iyya mai rike da mukamin gwamna ce ke lashe zaben kananan hukomomi a Najeriya?Meye tasirin hakan game da fatan da ake da shi na ganin cewa al’umma ta morewa tsarin dimokuradiyya daga tushe?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a