Kasuwanci

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:53:00
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.

Episodios

  • Yadda gwamnan CBN ya kashe naira biliyan 60 wajen siyen motocin alfarma

    04/09/2024 Duración: 10min

    Shirin "Kasuwa akai miki dole" tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin Babban Bankin Najeriya CBN na sayen motocin sulke na katsaita guda shida da ƙudin su ya haura naira biliyan 60, wanda gwamnan bankin da mataimakansa za su yi amfani da su, daidai lokacinda ƴan ƙasar ke fama da tsananin tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

  • Tasirin da tsarin musayar zinare ga makamashi ya yi ga tattalin arzikin Ghana

    28/08/2024 Duración: 09min

    Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya waiwayi shirin  gwamnatin Ghana na ban gishiri in baka manda a musayar zinare da man fetir, duk dai a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na haɓaka tattalin arziƙinta. Tun a bara ne gwamnatin na Ghana ta ƙaddamar da tsarin na ban gishiri in baka manda, wanda ta ƙarbi tan dubu 40 na man disel da ƙudinsu ya kai dala miliyan 40 wajen musanya da zinare da ƙasar ke da arzikinsa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

  • Masu sana'ar kifi a Najeriya sun koka kan tsadar abincin kiwo

    21/08/2024 Duración: 10min

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba yadda kasuwancin kifi a Najeriya ya ke neman ya gagari masu sana’ar saboda tsadar abincin da ake kiwon kifi da shi da farashin sa ya ƙaru, lamarin da ke barazana musamman ga ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa a fannin. Farashin buhun abincin kifi ya tashi daga N18,000 a shekarar 2023 zuwa N36,000 a wannan shekarar, wanda ya nuna karuwar kashi 100 cikin 100 a fadin Najeriya.Wannan al’amari ya yi kamari a yankin Neja Delta da suka yi kaurin suna a noman kifi.

  • Najeriya ta yi asarar sama da naira triliyan 5 a zanga-zangar kwanaki 10

    14/08/2024 Duración: 09min

    Shirin Kasuwa A kai miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya tattauna irin asarar da aka yi a Najeriya sakamakon zanga zangar kwanaki 10 da ƴan ƙasar suka yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari. Ministar masana’antu da Kasuwanci da kuma zuba jari na kasar Dr. Doris Uzoka Anite ta ce, alkakuma da suka tattara na wucin gadi, sun nuna cewa Najeriya ta yi asarar naira biliyan 500 a duk rana ta Allah yayin zanga-zangar, bayaga dukiyar da aka barnata ta hanyar kone-kone ko sata da makamanci hakan da takai naira biliyan 52, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

  • Yadda basuka su ka yi wa ƙasar Ghana katutu a cikin shekara guda

    07/08/2024 Duración: 09min

    A yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024.Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024. A cewar babban bankin na Ghana, bashin da ake bin ƙasar ya karu ne zuwa Cidi biliyan 658.6 a watan Fabrairun wannan shekarar, tsabanin Cidi biliyan 611.2 da yake a ƙarshen shekarar 2023.

  • Yadda Najeriya ke fuskantar tashin farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 30

    24/07/2024 Duración: 10min

    A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata. Shin ko hakan zai kawo sauƙi kan halin da ake ciki a ƙasar? Kuna iya latsa alamar sauti don jin amsar wannan tambaya tare da masana ta cikin shirin...

  • Gwamnatin Najeriya za ta yi odan abinci daga waje saboda tsadar rayuwa a ƙasar

    17/07/2024 Duración: 10min

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin gwamnatin Najeriya na sahale shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa da wake da alkama da masara ba tare da biyan ƙudin fito ba har tsawon watanni 5, domin rage tasirin tsaɗar kayan abinci da ƴan ƙasar ke fama da shi tun bayan ɗarewar shugaba Bola Ahmed Tinubu mulki a bara. A wani taron manema labarai da ya kira wannan Litinin, ministan noma da samar da abinci na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana sabon matakin, inda ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ƙudin fito da kuma haraji kan muhimman kayan abincin ne har na tsawon kwanaki 150, domin wadatuwar kayan a Najeriya.Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ƴan kasuwa masu bukatar shigo da kayan abinci, ita kanta gwamnatin tarayya za ta shigo da alkama da Masara kimanin tan dubu 250 kowanensu, domin bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.

  • Yadda gwamnatin Nijar ta saukaka farashin shinkafa ga al'ummar kasar

    03/07/2024 Duración: 09min

    Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali kan yadda gwamnatin Jamhuriyar  Nijar, ta fara saidawa talaka shinkafa a farshi mai rahusa, domin saukakawa ƴan kasar radadin matsin tattalin da suke ciki sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi. A ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Nijar ta hannun ma’aikatar kasuwanci ta kaddamar da wannan shirin,  inda ake sayar da buhu mai nauyin kilo 23 kan jaka 13 da rabi maimakon jika 17 zuwa jika 19 da ake sayar da shi a a wasu wurare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

  • Lokaci ya yi da Najeriya za ta rinka fitar da manja kasashen waje - Ƙungiyoyi

    26/06/2024 Duración: 09min

    Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali da kan kiranda wasu kungiyoyi suka yi wa gwamnatin Najeriya da ta yi wa Allah ta farfado da harkokin noma da sarrafa manja kamar yadda aka san ƙasar a baya. Kungiyar ɗalibai ta ƙasar ta yi  kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya farfado da harkokin sarrafa manja da Allah ya wadata ƙasar da shi, ta yadda hajar zata wadata ƴan Najeriya da ma fitar da shi ƙasashen waje kamar yadda lamarin yake a baya. Kirin ƙungiyar ta NANS na zuwa ne bayan da Shugaban ƙungiyar masu samar da manja ta Najeriya Mista Alphonsus Inyang, ya ce Najeriya na kashe sama da daka miliyan 600 duk shekara wajen shigo da Manja daga katare duk da cewa Allah ya albarkaci ƙasar da kwakwan Manja.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

  • Kasuwar kayan abincin da ake samarwa a dakunan kimiyya na sake samun karbuwa

    29/05/2024 Duración: 10min

    Shirin na wannan mako ya duba yadda kayan abinci da ake samar wa a kimiyyance maimakon shuka ko yanka dabbobi ke kara budewa. Danna alamar saurare tare da Ahmad Abba

  • Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da ta'azzara a Najeriya

    22/05/2024 Duración: 10min

    Shirin zai maida hankali ne kan hahoton baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar wanda ya bayyana yadda kasar ke ci gaba da fuskantar karin hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci, mafi muni da kasar ta gani a sama da shekaru 20. Rahoton wanda National Bureau of Statistic ta fitar a makon da ya gabata, ya cewa an fuskacin hauhawan farashin kayayyaki da sama da kashi 33 da rabi cikin 100 a watan Afrilun da ya gabata.

  • CAC a Najeriya ta bai wa masu sana'ar POS wa'adin watanni biyu su yi ragista

    15/05/2024 Duración: 11min

    Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya bukatar masu sana'ar POS da sauran masu mu'amala da na'urar da su garzawa hukumar rajistan kamfanoni ta kasar domin yin ragista kafin ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara ta 2024.

  • Yadda wani kamfanin kasar Denmark ya shirya zuba jarin dala biliyan 6 a Najeriya

    08/05/2024 Duración: 09min

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan mako ya mayar da hankali kan shirin wani kamfanin Denmark na zuba jarin kudi dala biliyan 6 a fannin tashoshin jiragen ruwan jihar Lagas ta Najeriya Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba

  • Dambarwar EFCC da wasu jiga-jigan tsohuwar gwamnatin Najeriya kan badakalar kudi

    01/05/2024 Duración: 10min

    Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matakin hukumar da ke yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annti EFCC na kaddamar na farautar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da kuma binciken wasu tsoffin mukarraban gwamnatin da ta shude kan cin hanci da rasha da kuma rufta da ci da dukiyar al’umma. A Najeriya, cikin ‘yan makonnin baya-bayan nan kusan za’a iya cewa hankulan al’ummar ƙasar sun karkata ne kan matakan da hukumar EFCC ke dauka kan wasu tsaffin jjiga-jigan gwamnatin da ta gabata, inda hukumar ta tsare kuma take shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman ƙasar ƙarkashin tsohon shugaban ƙasa Mohammdu Buhari, wato Hadi Sirika, bisa zargin almundahana na ƙudi da suka kai sama da naira biliyan takwas.Yayin da a bangare guda, aka shiga wasan buya da cece-kuce tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello da ke cewa abi umurnin kotu kan shirin kamashi yayinda shugaban hukumar ta EFCC ke cewa tabbas zai yi murabus muddun tsohon gwamnan bai g

  • Koken 'yan Najeriya na rashin saukar farashin kayan masarufi duk da faduwar Dala

    24/04/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce lamaarin ya yi muni. Ko da ya ke a wasu manyan biranen Najeriya irinsu Legas da Abuja, an fara ganin sauƙi a wasu kayayyakin abinci irinsu shinkafa da man girki da dai sauransu.Ku latsala alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba........

  • Yadda matasa suka rungumi kananan sana’o’i lokacin azumin Ramadana a Damagaram

    03/04/2024 Duración: 09min

    Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......

  • Gidauniyar Dangote ta kashe naira biliyan 15 na tallafin abinci a Najeriya

    27/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan rabon tallafin abincin naira biliyan 15, da Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar a Najeriya. Wannan dai na daga cikin matakan rage radadin talauci a tsakanin al'ummar Najeriya, da gidauniyyar hamshakin attajirin Afirka ta kaddamar a birnin Kano da ke arewacin kasar. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......

  • Yadda matsin rayuwa ya tilastawa 'yan Najeriya fasa rumbunan abinci

    06/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al’umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.

  • Yadda al'ummar kasashen yammacin Afrika ke kokawa saboda tsadar rayuwa

    28/02/2024 Duración: 09min

    A wannan makon shirin Kasuwa akai miki dole, zai yi duba ne game da bakar ukubar da al’ummar kasashen Nahiyar Africa ke fuskanta, a sanadiyar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, musamman kasashen Nijeriya, Nijar da kuma Cameroon. Yanzu haka dai a iya cewa wannan yanayi na hauhawar farashin kayan masarufi tuni ya zame wa kasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da kuma Cameroon Dan zani a kasuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.....

  • Yadda Najeriya ke neman taimakon Bankin Duniya don farfado da tattalin arziki

    13/02/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa a kai miki dole tare da Rukayya Abba Kabara a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Najeriya ke neman taimakon bankin duniya a wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin kasar da ke fuskantar tarnaki. Tattalin arzikin na Najeriya na ci gaba da durkushewa ne duk da kasancewarta mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika, dalilan da ake alakantawa da yankewar yawan man da kasar ke fitarwa baya ga ci gaba da zangewar darajar kudin kasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

página 1 de 2