Wasanni

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:59:29
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Episodios

  • Sharhi kan wasannin dab dana kusa dana ƙarshe a gasar zakarun Turai

    20/04/2026 Duración: 10min

    A makon daya gabata ne aka kammala wasannin zagayen dab dana kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda Bayern Munich ta cire Real Madrid, Atletico Madrid ita kuma ta doke Barcelona, Arsenal ta fidda Sporting CP, yayinda PSG ita kuma ta samu galaba kan Liverpool. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............

  • Matakan da CAF ke dauka don warware dambarwar da ke tsakanin Morocco da Senegal

    13/04/2026 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saley ya yi duba akan dambarwar da da ta taso dangane hukuncin karɓe nasarar Senegal ta lashe kofin Afrika na baya bayan da hukumar CAF tayi tare da maida nasarar ga ƙasar Morocco Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........

  • Hasashe game da rawar da ƙasashen Afirka za su taka a gasar lashe Kofin Duniya

    06/04/2026 Duración: 10min

    Shirin a wannan lokaci tare da  Khamis Saleh ya yi duba ne kan yadda aka kammala samun tawagogin ƙasashen da za su fafata a gasar lashe kofin duniya da ke tafe a watan Yuni mai zuwa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

  • Amurka ta gargaɗi masu aniyar maƙalewa idan suka je kallon gasar cin kofin duniya

    09/03/2026 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wassani a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda Amurka ta fara gargaɗin ƴan Ghana da ke da aniyar maƙalewa idan suka je ƙasar don kallon gasar cin kofin duniya da ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi baƙunci a watan Yuni mai zuwa. Ganin irin matakan da dama gwamnatin Amurka ke ɗauka kan shigar baki ƙasar tuni ofishin Jakadancin ƙasar da ke Ghana ya fara gargaɗin masu shirin halartar gasar da su guji wuce wa’adin da aka basu. Jakadan Amurka a Ghana Rolf Olson ya ce saɓawa dokokin shige da fice na ƙasar na iya haifar da mummunan sakamako, gami da rashin sake samun damar shiga ƙasar a nan gaba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............

  • FIFA za ta jagoranci koyar da ƙwallon ƙafa a makarantun Nijar

    02/03/2026 Duración: 09min

    Shirin “Duniyar Wasanni” tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda aka sanya tsarin koyar da wasan kwallon ƙafa a makarantun Boko na Jamhuriyar Nijar. A wannan makon mun yi dubi ne kan shirin koyar da wasan kwallon ƙafa da za a sirka a tsarin koyarwa a makarantun Boko a Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin da ake yi na haɓɓaka harkar, ganin  yanda take a baya sosai a jadawalin ƙasashe da hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA ta fitar inda Nijar ɗin ta ke a mataki na 111. Shi dai wannan tsarin, ya kasance wani shiri ne na haɗin gwiwa da aka yi tsakanin hukumar FIFA da kuma gwamnatin Nijar wanda hukumar kwallon kafa ta ƙasar fenifoot ke kula da shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda ta wakana a gasar tseren dawaki da ta gudana a garin Daura na jihar Katsina

    23/02/2026 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a garin Daura da ke jihar Katsina da ke a arewacin Najeriya. A farkon watan Faburairun wannan shekarar ne aka kammala babbar gasar tseren dawaki ta ƙasa da ƙasa da ƙungiyar sukuwar dawaki ta Najeriya ke shiryawa. Wannan ne dai karo na uku da ake gudanar da irin wannan sukuwa a cikin wannan shekarar, bayan da aka yi ta farko a birnin Katsina sai garin Hadeja na jihar Jigawa ya karbi bakunci sannan aka kamma sukuwan zangon farko na wannan shekarar a Daura. Mahaya daga Jihohin Kano da Sokoto da Neja da Bauchi da Kebbi da Katsina, waɗansu daga Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Mali da Chadi da kuma Burkina Faso, suka halarci gasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Taƙaddamar da ta dabaibaye gina filin wasa a jihar Kebbi ta Najeriya

    16/02/2026 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako, ya mayar da hankali ne kan taƙaddamar da ta dabaibaye gina filin wasa a jihar Kebbi ta arewacin Najeriya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh...

  • Gasar tseren dawakai da aka gudanar a jihar Jigawan Najeriya

    26/01/2026 Duración: 09min

    Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya.

  • Senegal ta lashe gasar AFCON karo na biyu bayan nasarar da ta samu kan Morocco

    19/01/2026 Duración: 09min

    A jiya Lahadi ne dai aka buga wasan ƙarshe a gasar lashe kofin nahiyar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ta karɓi baƙunci, inda Senegal ta samu nasara da ci 1 da nema kan Morocco, bayan da ɗan wasanta Pape Alassene Gueye ya jefa kwallo jim kaɗan bayan ƙarin lokacin. Wasan ƙarshen ya kasance mai cike da cecekuce sakamakon tsaiko minti 20 da aka samu, sanadiyar bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka bai wa Morocco, lamarin da ya fusata ƴan wasan Senegal ficewa daga fili, amma daga baya Sadio Mane ya dawo da su aka ci gaba da fafatawa. Ɗan wasan gaba na Senegal Sadio Mane ne ya lashe gwarzon ɗan wasa a wannan gasa, Yassine Bounou na Morocco ya lashe gwarzon mai tsaron raga shima abokin wasansa Brahim Diaz da ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida ya lashe kyautar takalmin zinari da kwallaye 5. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............

  • Super Eagles ta nuna bajinta a wasan ta da Aljeriya a gasar AFCON

    12/01/2026 Duración: 09min

    Shirin  Duniyar Wasanni na wanan mako tare da Khamis Saley ya yi  dubi kan nasarar da tawagar Najeriya ta samu a wasan dab da na kusa da na ƙarshe a gasar AFCON da ake gudanarwa a kasar Morocco. Shiga alamar sauti domin sauran cikakken shirin.....

  • Yadda aka doka wasu daga cikin wasanni ƴan zagayen 16 a gasar AFCON

    05/01/2026 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda  aka dawo da buga wasanni a zagayen ƴan 16 a gasar AFCON da ke gudana a Morocco a karshen mako. a Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......

  • An kammala gasar kokowa ta ƙasa mafi girma a Jamhuriyyar Nijar

    29/12/2025 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda aka kammala gasar kokuwar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar. Jiya Lahadi ne aka kammala gasar kokowar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar da aka gudanar a garin Tawa, wacce ita ce karo ta 46, inda mai masaukin baki ta lashe takobin bayan ƴan kokowarta biyu sun kai wasan ƙarshe a wannan gasa. Bayan karawa ta mintuna 11 da daƙiƙu 6, Nura Hassan ne ya yi nasara kan Zakiru Zakari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda aka yi bikin buɗe gasar cin kofin Afrika ta AFCON a Morocco

    22/12/2025 Duración: 09min

    Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zay yi duba ne kan yadda aka faro gasar lashe kofin nahiyar Afrika da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci. A daren jiya lahadi ne dai aka buɗe gasar lashe ƙofin nahigar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci. An dai buga wasanni tsakanin Morocco da Comoros, inda Moroccon ta samu nasasara da ci 2 da nema, wani abu da ke nuna cewa  ta faro gasar da ƙafar dama, bayan da Yariya Moulay Hassan bin Mohammed ya buɗe ta tare da rakiyar shugaban hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA Gianni Infantio da kuma shugaban hukumar kwallon ƙafar Afrika CAF Patrice Motsepe. Ɗan wasan gaba na tawagar Morocco Brahim Diaz da ke bugawa Real Madrid ne ya fara jefa kwallo a raga a minti na 55, kafin Ayoub El Kaabi na ƙungiyar Olympiacos da ya shigo daga baya ya ƙara a minti na 74. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Taƙaitaccen tarihi kan yadda aka faro gasar AFCON a shekarar 1957

    15/12/2025 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya yi duba ne kan tarihin gasar lashe kofin Afrika AFCON da hukumar CAF ke shiryawa. An faro buga gasar lashe kofin nahiyar Afirka, wacce ke zaman gasar kwallon ƙafa mafi girma da daraja a nahiyar a shekarar 1957, da hukumar kula da kwallon ƙafar Afrika CAF ce ta jagoranci. An fara gudanar da gasar ne a watan Fabrairun shekarar 1957 a birnin Khartoum na ƙasar Sudan da ƙasashe 3, kafin a shekarar 2019 aka faɗaɗata zuwa tawogogun ƙasashe 24, kuma Masar ce ta fara lasheta bayan lallasa Sudan da ta karbi baƙunci a wasan karshe, inda ta lashe kofin da aka sanya masa sunan Abdel Aziz Abdallah Salem, ɗan ƙasar Masar da ya fara shugabantar hukumar CAF. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda aka gudanar da jadawalin gasar cin kofin duniya ta 2026

    08/12/2025 Duración: 10min

    Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda rabon jadawalin gasar lashe kofin duniya da za a yi a baɗi ya gudana. A makon da ya gabata ne Hukumar Kula da Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ta fidda jadawalin Gasar Kofin Duniya na shekarar 2026, wacce za ta gudana a tsakanin ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico. Bikin dai ya gudana a cibiyar Kennedy da ke birnin Washington DC, ƙarƙashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban FIFA Gianni Infantino.

  • Matsalar da hukuncin ɗauke wasan Kano Pillars da Katsina Utd a gida ya ja musu

    01/12/2025 Duración: 10min

    Shirin awannan mako zai duba batun hukuncin ɗauke ƙungiyoyin Kano Pillars da Katsina United daga buga wasannin sun a gida a gasar NPFL ta Najeriya, da hukumar da ke shirya gasar ta yi. Kamar yadda masu bibiyar gasar Firimiyar Najeriya suka sani ne a baya bayannan, Hukumar Shirya Gasar NPFL ta Najeriya ta ɗauki hukuncin dakatar da manyan ƙungiyoyin arewacin Najeriya biyu wato Kano Pillars da Katsina United daga buga wasannin su na gida, inda aka maida Pillars buga wasan ta a Jihar Katsina, yayin da ita kuma Katsina United aka mayar da ita buga wasannin ta a jihar Pilato.

  • Yadda Ashraf Hakimi ya lashe gwarzon shekara na Afrika karon farko

    24/11/2025 Duración: 09min

    Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafan Afirka da Achraf Hakimi na Morocco ya lashe. A makon daya gabata ne Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF, ta bayar da kyautuka ga zaratan ƴan wasan nahiyar da suka nuna bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. A yayin bikin da ya gudana a birnin Rabat na ƙasar Morocco, hukumar ta CAF ta sanar da ɗan wasan baya na tawagar ƙasar ta Morocco wanda kuma ya ke yi wa ƙungiyar PSG wasa Achraf Hakimi,  a matsayin wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka a wannan shekarar. Hakimi ya samu nasarar ce bayan doke shahararrun ƴan wasan nahiyar da suka taɓa lashe kyautar irinsu Mohamed Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool,  da kuma Victor Osimhen na Nigeria da ke wasa a Galatasaray. Wannan ne dai karo na farko da ɗan wasan ya taɓa lashe ƙyautar, bayan da a karo biyu a jere ya na ƙarewa a mataki na biyu, a shekarar 2023 da Victor Osimhen ya lashe da kuma 2024 da Ademola Loo

  • Yadda ta kaya a karawar da aka yi tsakanin Najeriya da DR Congo

    17/11/2025 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda wasan ƙarshe na nemon gurbin wakiltar Afrika a matakin duniya, wajen samun tikin zuwa gasar lashe kofin duniya ya gudana tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Dimukaraɗiyyar Congo. Karawar da suka yi a filin wasa na Moulay Abdellah da ke birnin Rabat, ta kai matakin dugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da suka tashi 1-1.   Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............

  • Yadda aka fafata a gasar kofin Sardauna ta tsoffin 'yan wasan arewacin Najeriya

    10/11/2025 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako ya mayar da hankali ne kan gasar da tsofaffin ƴan wasan Najeriya da suka fito daga jihohin Arewacin ƙasar suka fafata. A makon daya gabata ne garin Maiduguri babban birnin jihar Borno, ya karɓi baƙuncin gasar kofin Sardauna karo na 13, wacce tsofaffin ƴan wasan da suka fito daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya suka ƙirƙira da zummar sada zumunci da kuma haɗa kan jihohin arewacin ƙasar. Tawagar da ta wakilci jihar Kebbi a wannan gasa ce dai ta yi nasarar lashe wannan kofi, bayan da ta doke takwararta ta Kano a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci 4-3. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh...

  • Karo na biyu a jere Alƙalan wasan Najeriya sun gaza samun wakilci a AFCON

    03/11/2025 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda Najeriya ta gaza samun gurbin alƙalin wasanni a gasar AFCON karo na biyu a jere. A ƙarshen watan da ya gabata ne hukumar ƙwallon ƙafar Afrika CAF ta fitar da jadawalin alƙalan wasanni da za su bayar da gudunmawa a gasar cin kofin ƙasashen Afrika ta AFCON da zata gudana a Morocco cikin watan gobe, amma ba tare da alƙalin wasa ko guda ɗaya daga Najeriya ba. Ko a makamanciyar gasar da ta gabata a Ivory Coast cikin shekarar 2024 babu wakilcin ko da alƙalin wasa guda daga Najeriyar, lamarin da ke matsayin babban koma baya ga wannan ƙasa ta tayi shura a fagen ƙwallo. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

página 1 de 2