Lafiya Jari Ce

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:38:44
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.

Episodios

  • Yawaitar masu fama da lallurar laka a sassan Najeriya

    16/09/2024 Duración: 09min

    A wannan mako shirin zai mayar da hankali game da cuta ko kuma ‘‘lalurar katsewar Laka’’ wato Spinal cord Injury, lalurar da a baya-bayan nan alƙaluma ke nuna yawaitar masu fama da ita a sassan Najeriya, walau sakamakon haɗarin mota ko rikici dama sauran dalilai. Yayin bikin ranar wayar da kai game da lalurar ta Laka da ke gudana a kowanne wata na Satumba, da a wannan karon aka yiwa take da ‘‘ Kawar da tarzoma a matsayin hanyar kawar da laka’’ masana sun ce baya ga haɗurran mota hanyoyi da dama na haddasa wannan lalura ta laka.

  • Yadda cutar borin gishiri ke addabar mata masu juna biyu a Jamhuriyar Nijar

    09/09/2024 Duración: 10min

    A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan cutar borin gishiri ko kuma kumburin da mata ke fama da ita yayin da suke da dauke da juna biyu, wacce kuma a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. Wannan cuta a Jamhuriyar Nijar na daga cikin wacce ke ciwa hukumomi tuwo a kwarya ganin yadda mata sama da dari biyar da 30 cikin kowace mace dubu daya ne kamuwa da wannan cuta, kuma sama da 50 ke rasa ransu a sanadiyarta.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Ƙaruwar ƙananan yara da ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki

    02/09/2024 Duración: 10min

    A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan ƙaruwar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa ko kuma Tamowa a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci, cikinsu kuwa har da Nijar, ƙasar da alƙaluman 2021 ke cewa akwai ƙananan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 akalla miliyan 1 da dubu 800 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. A baya-bayan nan anga ƙaruwar yaran da ke fama da cutar Tamowa ko da ya ke har yanzu akwai ƙaranci sani game da cutar, kan hakan mu ka fara da tuntuɓar Dr Fayuz Mu’azu likitan mai kula da ƙananan yara masu fama da cutar Tamowa a jihar Diffa, ya kuma yi mana bayani kan cutar da dalilan da ke haddasata.

  • Hatsarin da ke cikin amfani da maganin ƙwari wajen adana kayan abinci

    22/07/2024 Duración: 09min

    Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani da ma sshigowa da shi Najeriya, bayan da ce bincikenta ya tabbatar  da cewa maganin yana haddasa cutuka da suka haɗa da cancer.

  • Tasirin sabbin abinci da aka ƙirƙira wato Synthetic Foods ga lafiyar jama'a

    15/07/2024 Duración: 09min

    Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan tasarin nau'ukan abinci da akan ƙirkira a ɗakunan bincike wadanda ake kira Synthetic foods a turance, domin nazari kan illolinsu ko kuma akasi ga lafiyar jama'a, duba da yadda nau'ukan abinci da nomansu akayi ba ko kiwo ke samun ƙarbuwa a wasu kasashen duniya.

  • Yadda cutar kansar bakin mahaifa ke hallaka mata a tarayyar Najeriya

    01/07/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi duba ne kan yadda kansar bakin mahaifa ke hallaka Mata, musamman ƴan tsakanin shekaru 15 zuwa 44, a Najeriya. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron shirin...

  • Yadda mata ke rungumar tiyatar gyaran jinki duk da gargadin da likitoci ke yi

    24/06/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba kan yadda mata ke yin tiyatar gyaran jiki ko sauya sura wato Cosmetics Surgery, wacce a yanzu mata da dama suka runguma, duk kuwa da yadda likitocin ke ganin hakan na da illa ga lafiyarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

  • Tsarin kiwon lafiya da mahukunta ke dauka a Saudiyya

    10/06/2024 Duración: 10min

    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba yanayin lafiyar mahajjata, a dai-dai lokacin da al'ummar Musulmai ke gudanar da ibadar hajji a Saudiyya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu

  • Har yanzu 'yan Najeriya da dama basa cin gajiyar shirin Inshorar lafiya -Bincike

    03/06/2024 Duración: 09min

    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al’ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama’a samun kulawar lafiya cikin rahusa, lura da yadda kaso mai yawa na al’ummar ƙasar ke rasa kudaden iya kai kansu ga likitoci ko da suna cikin matsananciyar cuta.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

  • Yara 'yan kasa da shekaru biyar na gaza samun alluran rigakafin da ta dace

    27/05/2024 Duración: 09min

    Shirin na wannan mako ya duba yadda kananan yara musamman a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa ke gaza karbar alluran rigakafin da ya kamata su samu kafin cika shekaru biyar da haihuwa.

  • Halin da ake ciki a yaki da cutar yunwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar

    20/05/2024 Duración: 09min

    A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya yi duba ne a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Tamuwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar.

  • Bayani a kan cutar ƙyanda da yadda za a kare yara daga kamuwa

    13/05/2024 Duración: 09min

    A wannan makon shirin zai yi duba kan cutar kyanda ko kuma measles a turance, cutar da galibi akan ga bullarta a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin zafi musamman a yankunan kasashen yammacin Afrika Sahel.  Zuwa karshen watan Fabarairun da ya gabata, fiye da yara 700 suka harbu da cutar kyanda a jihar Borno cikin watan yayinda zuwa yanzu ta kashe kananan yara 42 a jihar Adamawa yayinda wasu fiye da dubu guda suka harbu.Bari mu bude da rahoton wakilinmu Ahmad Alhassan daga jihar Adamawa, jihar da zuwa yanzu tsanantar wannan cuta ta kyanda ta tilasta kulle makarantu.

  • Yadda matasa ke rungumar tsarin yin kaho a zamanance

    06/05/2024 Duración: 10min

    Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tsarin yin kaho a zamanance Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu

  • Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru

    03/05/2024 Duración: 10min

    Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai. Tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha na  matsayin ginshikin lafiyar jama’a wanda kuma rashin ke matsayin babbar barazanar bullar tarin cutuka na cikin wajen jikin bil’ada, sai dai samun ruwan sha ko na amfani ga galibin al’ummomin da ke rayuwa a yankin arewacin Kamaru na matukar wahala.A baya-bayan nan al’ummar yankin na ganin bullar cutuka da dama masu alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha ko na amfani, yankin da kashi 43.5 na al’ummarsa ne kadai musamman mazauna karkara kan iya samun wadatacce kuma tsaftataccen ruwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.

  • Amfanin Azumi ga lafiyar jikin dan Adam

    01/04/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne game da alfanun Azumi ga lafiyar jikin dan Adam. Masana kiwon lafiyar dai na bayyana cewar Azumi na taimakawa wajen rage kaifin wasu cutuka a jikin dan adam. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Yadda ya kamata mai Azumi ya kula da kansa a lokacin zafi

    25/03/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan irin cutukan da ke karuwa a lokutan Azumi musamman yadda a wannan karon ake gudanar da ibadar a cikin yanayi na tsananin zafi, wanda masana ke ganin akwai wasu naukan cutukan da ka iya bijorowa. Masana kiwon lafiya dai sun gargadi masu dauke da wasu nau'ukan cutuka kan irin matakan da ya kamata su dauka don kula da lafiyarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Yadda aka yi wa sama da yara dubu dari 9 rigakafin cutar Polio a Kamaru

    18/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gangamin rigakafin cutar shan inna wato Polio a Jamhuriyar Kamaru don dakile bazuwarta. A baya-bayan nan ne dai ake ganin bullatar cutar a wasu sassan kasar, lamarin da ya sanya mahukunta tashi tsaye don yin rigakafin cutar. Sama da yara dubu dari 9 da 48 ne aka yi wa rigakafin a fadin jahohi 10 na Kamaru, a aikin da aka kwashe tsawon kwanaki uku ana yi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Yadda maza a Najeriya ba sa bai wa gwajin sankarar mafitsara mahimmanci

    04/03/2024 Duración: 10min

    A wannan mako shirin ya mayar da hankali kan nau’ikan cutakan da ba a fiya mayar da hankali wajen yakarsu ba musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya, wannan nau’in cutuka kuwa sun kunshi kansar mafitsara ko kuma Prostate Cancer, nau’in kansar da ke matsayin mafi hadari ga maza, amma kuma ba ta samun kula duk da yadda ta ke kisan akalla mutum dubu 8 duk shekara a Najeriya. 

  • Yadda ake samun karuwar masu kamu wa da cutar cizon mahaukacin kare a Najeriya

    26/02/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan cutar cizon mahaukacin kare ko kuma Rabies a turance, bayan da bincike ya nuna cewar cutar na karuwa a Najeriya duk da cewa babu cikakkun alkaluman wadanda cutar ta shafa saboda karancin kawo rahoton cutar ga mahukunta. Sai dai wasu alkaluman hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriyar NDDC sun nuna cewa daga shekarar 2017 zuwa 2022 akwai akalla mutane 998 da kuma karnuka 273 da suka harbu da cutar ta Rabies ko kuma cizon mahaukacin kare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Cutar kazuwa ta addabi al'ummar wasu yankunan Jamhuriyar Nijar

    19/02/2024 Duración: 09min

    A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan cutar kazuwa ko kuma Smallpox a turance, cutar da ke sahun cutuka masu matukar hadari da ke haddasa kuraje masu matukar kaikayi da mashasshara da kuma hana barci, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kawar da ita daga ban kasa tun a shekarar 1980 amma kuma duk da haka ake ganin bullarta lokaci zuwa lokaci. Cutar ta kazuwa wadda ake alakantawa da kazanta a baya-bayan nan ne aka samu barkewarta a wasu kauyukan Jihar Maradi ta Jamhuriyyar Nijar, inda masana ke cewa zuwa yanzu akwai fiye da mutum dubu 3 da suka harbu, kuma kaso mai yawa na Almajirai da magidanta sai kuma kananan yara musamman a kauyukan Surori zuwa Tsibiri da kuma garin Udal, wanda ke matsayin karon farko da aka ga bullar cutar bayan shafe tsawon shekaru ba tare da jin duriyarta ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu....

página 1 de 2