Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:55:52
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodios

  • Ra'ayoyin masu saurare kan tsadar farashin litar fetur

    17/09/2024 Duración: 09min

    Ana iya cewa murna na neman komawa ciki a Najeriya, bayan da aka yi hasashen cewa da zarar Dangote ya fara shigar da tataccen mai a kasuwa zai wadata sannan akan farashi mai rahusa. To sai dai ranar farko da fara shiga da man na Dangote, sai kamfanin NNPCL ya sanar da ƙara farashin mai a kasar.Shin ko me za ku ce a game da wannan sabon karin faraashin mai wanda shi ne karo na uku cikin shekara daya a Najeriya?Ko meye dalili karuwar farashin mai a Najeriya duka da cewa ana hakowa da kuma tace shi ne a cikin gida?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan bikin maulidi

    16/09/2024 Duración: 10min

    Yanzu haka al’ummar musulmi a sassan duniya na ci gaba da gudanar da bukukuwan Mauludi, domin tunawa da ranar da aka haifi annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah. Shin ko yaya matsayin wannan rana yake a gare ku?Ta wace fuska ku ke gudanar da bikin tunawa da wannan ranar?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayoyi: Belin miliyan 10 kan masu zanga-zangar yunwa a Najeriya

    12/09/2024 Duración: 10min

    Kotu a Abujan Najeriya, ta bukaci 10 daga cikin ɗimbin mutanen da aka kama suna zanga-zanga domin yunwa, da ya biya Naira milyan 10 a matsayin kuɗin beli kafin sallamar sa daga gidan yari. Shin ko ta ina wanda ke fama da yunwa zai fito da Naira milyan 10 domin ya beli kansa?To me zai faru idan har wani ko wasu suka taimaka da waɗanda kuɗade ba beli?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan ambaliyar ruwa a Afrika

    11/09/2024 Duración: 10min

    Yamai babban birnin Jamhuriyar, ya fara karɓar baƙuncin taron ƙwararru da saurann masu ruwa da tsaki kan matsalar sauyin yanayi da ta shafe yankin yammacin Afrika. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sassan yankin na Yammacin Afirka da Sahel ke fuskantar Iftila’in Ambaliyar mafi muni da aka taɓa gani cikin aƙalla shekaru 20, kamar yadda aka gani a garin Maiduguri, inda a baya bayan nan saukar ruwan sama ya janyo tumbatsar dam ɗin da ya fashe, lamarin ya haddasa mummunar ambaliyar da ta mamaye sassan birnin da dama.Wane hali ake ciki a garin na Maiduguri bayan iftila’in da ya auku?Wadanne dabaru ya dace a bi wajen daƙile sake aukuwar haka, ko kuma rage girman barazanar da aka gani, ta hanyar karkatar da tarin ruwan da ke ambaliya zuwa ga amfanin jama’a?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin

  • Ra'ayoyin masu saurare kan buƙatar Katsinawa su tashi su kare kansu

    10/09/2024 Duración: 09min

    Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Malam Dikko Umaru Radda ya yi kira ga al’umma da ta jajirce wajen kare kanta daga hare-haren ƴan bindiga masu garkuwa da mutane, tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai don kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan komawa makarantun boko

    09/09/2024 Duración: 09min

    A Najeriya, yau ake sake buɗe makarantun firamire da sakandare don fara karatu bayan dogon hutu da aka gudanar. Ana komawa makarantar ne a wannan karo a cikin wani yanayi na matsanciyar tsadar rayuwa wanda ya samo asali daga sabon ƙarin farashin mai fetur da aka yi a kasar.Shin a wane yanayi yaranku ke komawa makarantar a wannan litinin?Ko akwai wani sauyi musamman ta fannin farashin kayan karatu da kuma kudin sufuri?

  • Ra'ayoyin Masu Saurare kan batutuwa daban daban

    06/09/2024 Duración: 10min

    RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinku kan batutuwa daban daban da ke ci musu tuwo a ƙwarya a kowacce ranar Juma'a.  Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan tasirin taron China da Afrika

    05/09/2024 Duración: 09min

    An fara taron shekara-shekara don kyautata hulɗa tsakanin China da Afirka wanda ya samo asali kimanin shekaru 24 da suka gabata.  Alƙaluma sun tabbatar da cewa China ita ce ƙasar da nahiyar Afirka ta gudanar da hulɗar tattalin arziki da kasuwanci fiye da kowace nahiya, yayin da a ɗaya bangare bashin da China ke bin Afirka ke ci gaba da ninkawa ninkin-ba-ninkin.Meye ra’ayoyinku a game da kamun lodayin China a fagen tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewa a nahiyar Afirka?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Alheri Haruna.

  • Yadda batun ci gaba da biyan tallafin mai a Najeriya ya janyo cecekuce

    20/08/2024 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan mako ya duba yadda ake fama da matsalar karancin main fetur a Najeriya, wasu bayanai na nuni da cewa yanzu haka gwamnatin ƙasar ta ware naira triliyan 6 da bilyan 800 a matsayin kuɗin tallafi mai a ƙasar.Bayanai sun ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne don biyan tallafin tun daga watan agustan bara har zuwa disambar wannan shekara ta 2024 wato wata watanni 17 cur. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara

  • Ra'ayoyin masu saurare kan gudummawar marigayi Issa Hayatou ga kwallon ƙafa

    12/08/2024 Duración: 10min

    A makon jiya ne Allah ya yiwa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afirka Issa Hayatou rasuwa, bayan gajeruwar rashin lafiya. Hayatou da ya kwashe kusan shekaru 30 yana jagorancin hukumar, ya taka rawa sosai wajen ci gaban kwallon kafa a nahiyar, musamman bangaren matasa da kuma ganin an kara wa kasashen Afirka gurbi a gasar cin kofin duniya daga gurabe 2 zuwa 5.Shin kun gamsu da gudumawar da ya bayar?Kamar da me za ku tuna wannan gwarzo?

  • Ra'ayoyin ƴan Najeriya kan jawabin shugaba Tinubu game da zanga-zanga

    05/08/2024 Duración: 09min

    Shugaban  Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su jingine zanga-zanga tare da bayyana aniyar tattaunawa don laluɓo masalaha. A jawabin da ya gabatar sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da ta ɓarke a akasarin sassan ƙasar, Tinubu ya shaida wa ƴan Najeriya cewa yana jin raɗaɗin da suke ji, kuma tabbas zai samo mafita.Yaya wannan jawabi nasa ya riske ku?Ko ya taɓo batutuwan da suke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya?Wace shawara za ku ba wa masu zanga-zanga?

  • Ra'ayoyin masu saurare kan shigar iyayen al'umma cikin ayyukan garkuwa da mutane

    30/07/2024 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya duba yadda rashin tsrao da kuma garkuwa da mutane ke kara yawaita a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan nan kwamishin yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya sanar da cafke 'dan majalisar dokoki da hakimi tare da tsohon shugaban karamar hukumar Kaurar Namoda bisa zarginsu da hannu dumu dumu cikin ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kuɗin fansa. Wannan al’amari ya sake tabbatar da zargin da ake yi wa wasu daga cikin shugabanni a Najeriya dangane da taka muhimmiyar rawa a matsalolin tsaron da suka addabi al’ummar ƙasar.Me za ku ce kan wannan lamari?Wane darasi ya kamata al’umma su koya?Wace mafita ce mafi dacewa a bi wajen magance matsalolin tsaron dake tagayyara jama’a?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare da Nasiruddeen Muhammad

  • Ra'ayoyin masu saurare kan karuwar hare-hare a kasashen Sahel da kewaye

    29/07/2024 Duración: 09min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi ke kara zafafa hare-hare a kasashen yankin Sahel. Hare-haren mayakan ya fara tsallakawa zuwa kasashen Jamhuriyar Benin da Togo wadanda basu saba ganin irin haka a kasashen su ba.Ina ne kuke ganin ya kamata mahukunta su kara azama don samun zaman lafiya mai dorewa?Wace gudunmowa zaku bayar a matsayinku na al'umma don tabbatuwar tsaro a kasashen ku?Wannan shine maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan dambarwar matatar Dangote da gwamnati

    23/07/2024 Duración: 10min

    Taƙaddamar da ta kunno kai tsakanin hamshaƙin attajirin nahiyar Afirka Aliko Dangote da kamfanin man Najeriya NNPCL na ƙara yin ƙarfi a ‘yan kwanakin baya bayan nan, bayan da yayi korafin da ya yi cewar ana yiwa matatarsa zagon kasa, yayin da kamfanin ya mayar da martanin cewar Dangote bashi da lasisi, kuma yana son gwamnati ta soke lasisin masu shigo da mai domin mallaka masa. A karshen mako ne dai Ɗangoten ya tallata wa Kamfanin NNPCL damar sayen sabuwar matatar tasa da ya kashe akalla dala biliyan 20 wajen gina ta ganin yadda dangantaka ke cigaba da yin tsami tsakaninsu.Me za ku ce kan wannan al’amari?Ta yaya za a ɗinke wannan ɓaraka?Wace shawara kuke da ita ga ɓangarorin biyu?

  • Ra'ayoyin masu saurare kan kwararar baƙin haure ta Libya zuwa Turai

    18/07/2024 Duración: 09min

    Wakilan ƙasashe 28 sun gana da mahukuntan Libya kan hanyar da za su bi wajen dakile matsalar kwararar dubban bakin hauren da ke tsallaka Teku don shiga nahiyar Turai. A shekarun baya bayan nan Libya ta zama babbar cibiyar da ‘yan ci rani daga Afrika ke bi wajen tsallaka teku zuwa Turai, inda alkaluma suka nuna cewar, daga farkon wannan shekara zuwa 5 ga watan Yulin da muke ciki, ‘yan cirani kimanin dubu 14 da dari 755 suka isa Italiya daga Libyan.Me ya sa wannan matsala ta kwararar yan ci rani daga Afrika zuwa Turai taki ci taki cinyewa duk da matakan da ake ɗauka?Ta yaya za a warware wannan matsala?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Mabanbantan ra'ayoyin masu saurare kan abubuwa da dama

    05/07/2024 Duración: 09min

    RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan abubuwa da dama ke ciki musu tuwo a kwarya a duk ranar Juma'a. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu

  • Ra'ayoyin Masu Saurare kan zaɓen Faransa

    02/07/2024 Duración: 04min

    Cikunan ƴan siyasa sun ɗuri ruwa a Faransa, bayan da masu tsattsauran ra’ayi suka lashe sama da 33% na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen shiga Majalisar Dokokin Ƙasar, tare da yiyuwar samun gagarumar nasara a zagaye na biyu na zaɓen da za a yi ranar Lahadi mai zuwa. Ana matuƙar nuna fargaba dangane da abin da zai faru matuƙar masu wannan ra’ayi suka samu rinjaye a majalisar, saboda tsauraran manufofinsu da suka haɗa da ƙyamar baƙi da kuma neman rage duk wani taimako da ake bai wa ƙasashe masu tasowa.Shin ko yaya kuke kallon wannan lamari da ke faruwa a fagen siyasar ƙasar ta Faransa?Wannan shi ne abin da shirin Ra'ayoyin Masu Saurare na wannan rana ya tattauna a kai.Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan ɓarkewar cutar kwalara a Najeriya

    27/06/2024 Duración: 09min

    Hukumar Yaƙi da Cututuka Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya, ta ce kawo yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar Amai da gudawa wato Cholera sun kai dubu 1 da 579, kuma tuni 54 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya. Hukumar ta yi gargaɗi ga jama’a da su kiyaye ta hanyar ɗaukar matakan kariya, domin kuwa tuni cutar ta shiga jihohi 32 na ƙasar.Waɗanne irin matakai mahukunta ke ɗauka a yankunanku domin hana yaɗuwar wannan cuta?A naku ɓangare, waɗanne matakai ku ke ɗauka domin kare kanku?Kuri ka aiko mana da  ra’ayoyinku a lambarmu ta WhatsApp +234 70 66 35 66 41 da kuma shafinmu na Facebook.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan ɓarkewar zanga-zanga a Kenya

    26/06/2024 Duración: 10min

    Yunƙurin ƙara haraji a kan kayayyakin masarufi, ya haddasa ɓarkewar mummunar tarzoma a Kenya, inda aka tabbatar da mutuwar mutane da dama a jiya labara musamman a birnin Nairobi. Shin ko meye ya yi zafi har wannan tarzoma ta ƙazance tare da samun asarar rayuka da kuma cinna wa wani ɓangare na ginin majalisar dokokin ƙasar wuta?Ko akwai wani darasi da ya kamata gwamnatocin sauran ƙasashe su ɗauka domin kauce wa fushin al’ummominsu?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin

  • Mabanbantan ra'ayoyin masu saurare kan abubuwa da dama

    21/06/2024 Duración: 10min

    RFI Hausa na bai wa masu saurare damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya a kowacce ranar Juma'a. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

página 1 de 2